Sin tana son kara yin hadin gwiwa tare da kasar Rasha wajen sa kaimi ga samun zaman lafiya a yankin da ma duniya
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a nan birnin Beijing a yau Talata cewa, a sabuwar shekarar nan, kasar Sin tana fatan kara himma tare da kasar Rasha, wajen gudanar da hadin gwiwa kan harkokin kasa da kasa, da samar da gudummawa ta sa kaimi ga samun zaman lafiya a yankin da take da ma duniya gaba daya.
Lu Kang na tsokaci ne game da batun da ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov ya yi a gun taron manema labaru da aka gudanar a ranar 15 ga wata, inda ya ce Rasha da kasar Sin na dagewa wajen hadin gwiwa kan manyan batutuwan duniya, ciki har da batun zirin Koriya da sauransu. (Zainab)