in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhun MDD ya gaza amincewa da kudurin da Rasha ta gabatar kan binciken harin guba a Syria
2018-04-11 09:25:49 cri

Kwamitin sulhu na MDD ya gaza amincewa da kudurin da Rasha ta gabatar dake neman hukumar haramta amfani da makamai masu guba ta gudanar da bincike kan harin guba da aka kai Douma na Syria.

Kasashe 5 da suka hada da Bolivia da Sin da Habasha da Kazakhstan da Rasha ne suka kada kuri'ar amincewa da kudurin, adadin da bai kai kasashe 9 da ake bukata ba, inda kasashe 4 da suka hada da Britaniya da Faransa da Amurka da Poland, suka kada kuri'ar kin amincewa, yayin da kasashe 6 suka kauracewa kada kuri'ar.

Jakadan Rasha a MDD Vassily Nebenzia, ya bayyana rashin jin dadinsa da sakamakon, yana mai bayanin cewa, daftarin maimaici ne na daftarin da kasar Sweden ta rabawa mambobin kwamitin a ranar Litinin da ta gabata.

Ya kuma zargi wasu mambobin kwamitin da kada kuri'ar kin amincewa saboda kawai Rasha ce ta gabatar.

Dab da za a kada kuri'a kan daftarin Rasha ne, jakadan Sweden a MDD Olof Skoog, ya nemi a dakatar da taron na kwamitin sulhu domin kara tuntubar juna. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China