in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Putin da Merkel sun amince su taimakawa kokarin warware rikicin Syria
2018-04-18 11:21:55 cri

Fadar Kremlin ta Rasha, ta ce shugaban kasar Vladimir Putin da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel sun tattauna ta wayar tarho, inda suka ce a shirye suke, su mara baya ga yunkurin diflomasiyya da na siyasa wajen warware rikicin Syria, ciki har da tattaunawar neman sulhu da aka yi a Astana da Geneva.

Wata sanarwa da fadar Kremlin ta fitar a jiya ta ruwaito shugaba Vladimir Putin na bayyana matakin da wasu kasashen yamma suka dauka kan Syria a baya-bayan nan a matsayin take 'yancinta na kasa, wanda ya saba da dokokin kasa da kasa, tare da lalata yiwuwar warware rikicin kasar.

Amurka da Birtaniya da Faransa sun kaddamar da wasu hare-haren makamai masu linzami kan Syria a ranar Asabar da ta gabata, suna masu ikirarin cewa, harin martani ne ga harin makamai masu guba da suke zargin sojojin Syria da kai wa birnin Douma.

Shugabannin biyu sun kuma jadadda muhimmanci dake akwai ga ayarin kungiyar OPCW mai haramta amfani da makamai masu guba ta duniya, na gudanar da binciken kwakwaf mai ma'ana.

A ranar Litinin da ta gabata ne, wakilan Birtaniya a kungiyar OPCW suka zargi Rasha da Syria da hana ayarin masu binciken shiga Douma. Zargin da Moscow ta musanta na cewa, kwararrun na OPCW ba su samu izinin shiga garin ba daga MDD, sakamakon harin makamai masu linzami da aka kai kasar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China