Ministan masana'antu da harkokin sadarwa na zamani na kasar Sin Miao Wei ya bayyana cewa, kasarsa za ta bunkasa ci gaban fasahar sadarwa na zamani tare da yada amfani da fasahar intanet cikin shekaru masu zuwa, a wani mataki na zama kasar da ke kan gaba a fannin fasahar Intanet a duniya nan da shekakar 2035.
Ministan wanda ya bayyana hakan yayin wani taron Intanet, ya ce kasar Sin za ta gina kanta a fannin fasahar Intanet nan da shekarar 2035, domin zama ja gaba a fannin intanet a duniya.
Ya ce, don ganin an cimma wannan burin, kasar Sin za ta kaddamar da jerin muhimman ayyukan da abin ya shafa, gudanar da bincike a muhimman fannonin kere-kere da kara daga matsayin fasahar Intanet.
Sauran fannonin sun hada da karfafa dokokin da suka shafi inganta kare muhimman bayanan jama'a da na yanar gizo, da karfafa samar da kayayyaki da bullo da dokokin da suka shafi hada-hada ta intanet da sauransu.(Ibrahim Yaya)