in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta sanar da kafa hukumar hadin kai ta raya cigaban kasa da kasa
2018-04-19 10:56:07 cri
A jiya Laraba gwamnatin Sin ta sanar da kafa hukumar hadin kai ta raya cigaban kasa da kasa a hukumance.

Sabuwar hukumar za ta dauki nauyin tsara dabaru da shirye shiryen bada taimako ga kasashen waje; da bada shawarwari da kuma tafiyar da harkokin dake da nasaba da ayyukan bada taimakon; da yin gyare gyare kan tsarin bada taimako ga kasashen waje; da kuma yin tsare tsare da duba yadda ake aiwatar da ayyukan bada taimakon na kasa da kasa.

Yang Jiechi, wakilin ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin (CPC), kana darakta kwamitin tsakiya mai kula da harkokin kasashen waje na CPC, ya bayyana cewa, sabuwar hukumar zata taimaka wajen tabbatar da zaman lafiyar duniya da kuma ingiza cigaban bil adama.

Yang ya ce, hukumar tana da matukar muhimmanci ga tsarin diplomasiyyar kasar Sin da kuma shawarar "ziri daya da hanya daya". (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China