in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin: shawarar "ziri daya da hanya daya" na da amfani ga jama'ar kasashen duniya
2018-04-18 20:13:37 cri
An gabatar da wani sakamakon nazari kan shawarar " ziri daya da hanya daya" na kasar Sin a kasar Amurka, wanda ya shaida cewa, kasar Sin ta gabatar da shawarar ne ba domin neman tabbatar da moriyar bangarori daban daban ba kawai, maimakon haka, kasar Sin na fatan habaka tasirinta ne a fannin siyasa, da kara jibge sojojinta a sauran wurare. Dangane da wannan zargi, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Madam Hua Chunying, ta furta a yau Laraba cewa, hakika shawarar "ziri daya da hanya daya" na samun karbuwa sosai a yankuna daban daban, kuma dalilin da ya sa haka, shi ne kasancewar shawarar za ta biya bukatun jama'ar kasashe daban daban, musamman ma a wannan zamanin da muke ciki. Saboda haka tabbas, shawarar na tare da wata makoma mai haske.

Jami'ar kasar ta Sin ta kara da cewa, kasar Sin tana kokarin gudanar da shawarar "ziri daya da hanya daya", bisa manufar "sanya bangarori daban daban su tattauna kan ko wane shiri tare kafin a fara aikin gina shi", da "gudanar da aikin gini tare", gami da "sanya abin da aka gina ya amfani kowa". Saboda haka, duk wani aikin da ake gudanarwa karkashin laimar shawarar, ana yinsa ne bisa ra'ayi daya, wanda bangarori daban daban suka cimma, da sanya kowane matakin da aka dauka ya zama a bayyane, wato ba tare da rufa-rufa ba. A cewar Madam Hua, kasar Sin ba za ta yaudari wani don samun moriyar siyasa ba, kuma ba za ta rungumi wasu gami da rufe kofa ga wasu ba. Haka zalika ba za ta tilastawa wata kasa yarda da shawararta ba.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China