in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin: Bai dace a sabawa ra'ayin mafi rinjayen jama'a ba
2018-04-18 20:14:39 cri
Game da batun ziyarar da shugabar yankin Taiwan Madam Cai Yingwen ta yi a kasar Swaziland, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Madam Hua Chunying ta furta yau Laraba a nan birnin Beijing cewa, kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, manufa ce ta al'umma mafi rinjaye, wanda ko alama bai kamata a saba ma ta ba. Saboda haka, a cewar Madam Hua, ana fatan kasar dake nahiyar Afirka wadda batun ya shafa, za ta fahimci daidaitaccen ra'ayin da aka yarda da shi a duniya, sa'an nan ta goyi bayan hadin gwiwar da ake yi tsakanin Sin da kasashen Afirka.

Madam Hua ta kara da cewa, kasar Sin daya ce tak a duniya, kana Taiwan wani yanki ne na kasar Sin wanda ba za a iya balle shi ba. Kaza lika gwamnatin jamhuriyar jama'ar Sin, ita ce halastacciyar gwamnati daya tak da ke iya wakiltar daukacin al'ummomin kasar Sin a duniya.

Wannan ra'ayi, an tabbatar da shi ne cikin wani kuduri na MDD, haka kuma shi ne ra'ayin da yawancin kasashen duniya suke yarda da shi, in ji jami'ar kasar ta Sin.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China