in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan wasan Super Eagles sun kai wasan karshe a gasar CHAN
2018-02-01 19:27:29 cri
Kungiyar kwallon kafar Najeriya dake taka leda a gida ta Super Eagles, ta yi nasarar doke takwararta ta kasar Sudan da ci daya da nema, a ci gaba da buga gasar cin kofin nahiyar Afirka na CHAN da ake gudanarwa.

Nasarar da Super Eagles din ta samu a wasan na yammacin jiya Laraba wanda aka buga a birnin Marrakech na kasar Morocco, ya ba ta damar kaiwa wasan karshe na wannan gasa.

A ranar Lahadi ne kuma kungiyar za ta buga wasan karshe da takwararta, kuma mai masaukin bakin gasar wato kasar Morocco, wadda tuni ta lallasa Libiya da ci 3 da 1 a wasan kusa da na karshe da suka buga.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China