in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan cinikin da za a yi ta intanet a tsakanin Sin da kasashen waje zai kai RMB Yuan biliyan dubu 12 a shekarar 2020
2017-11-27 10:28:06 cri
A kwanakin baya, an gabatar da sanarwar kwamitin kula da ka'idojin harajin kwastam na majalisar gudanarwar kasar Sin, inda aka bayyana cewa, tun daga ranar 1 ga watan Disamba na shekarar 2017, an rage wasu harajin kwastam na kayayyakin da ake shigar da su Sin ta hanyar tsara yawan haraji na wucin gadi.

A wannan karo, kayayyakin da aka ragewa harajin kwastam sun hada da abinci, da maganin gina jiki, da magunguna, da kayayyakin yau da kullum, da tufafi, da takalma da huluna, da na'urorin amfani na yau da kullum da dai sauransu.

Shugaban cibiyar nazarin ciniki ta intanet ta kasar Sin Cao Lei ya bayyana cewa, rage harajin kwastam zai sa kaimi ga sayar da kayayyakin kasar Sin, kana zai kawo moriya ga dandalin yin ciniki a tsakanin kasa da kasa ta hanyar intanet.

Hukumar bincike ta iResearch da ta OCN ta kasar Sin, sun yi hasashen cewa, a karkashin yanayin aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya", yawan ciniki a tsakanin Sin da kasashen waje ta intanet a shekarar 2017 zai kai RMB Yuan biliyan dubu 7, a kuma shekarar 2018 zai kai RMB Yuan biliyan dubu 8.8, yayin da a shekarar 2020 kuma ake hasashen zai kai RMB Yuan biliyan dubu 12. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China