in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jakadan kasar Sin a Amurka ya nuna rashin amincewa da matakan kariyar ciniki
2018-01-25 12:01:30 cri
Jakadan kasar Sin a Amurka Cui Tiankai a ranar 23 ga wata ya bayyana cewa, kasar Sin tana nuna rashin amincewa da matakan kariyar ciniki da aka dauka daga bangare guda, kuma tana da 'yancin daukar matakai na kare moriyar kanta bisa doka.

Mr. Cui ya fadi hakan ne a yayin da yake hira da Bill Sternberg babban editan jaridar USA Today, a game da yadda gwamnatin kasar Amurka ke sanya kudin kwastan masu yawa a kan kayayyakin kasar Sin.

Mr. Cui ya ce, Sin da Amurka suna samun moriyar juna daga huldar tattalin arziki da cinikayya da juna. Duk da matsalar da ake iya fuskanta a kan wasu batutuwa, amma kasashen biyu na alaka da juna sosai ta fannin tattalin arziki, misali yanzu da wuya mu tabbatar da cewa wani kaya kasar Sin ce ta samar ko kuma Amurka ta samar.

Mr. Cui Tiankai ya kara da cewa, kamata ya yi a daidaita matsalolin bisa tsarin cinikayya da ya hada da hukumar cinikayya ta duniya(WTO).

Daga karshe, Mr.Cui Tiankai ya ce, kasashen Sin da Amurka na kara fuskantar cikas da batutuwan siyasa ke kawo wa harkokin cinikayyarsu, abin da kuma ya jawo hankalinsu duka, kuma matakan kariyar ciniki da aka dauka ba za su taimaka ga daidaita matsalolin da aka fuskanta ta fannonin tattalin arziki da zaman al'umma ba.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China