in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabon firaiministan Habasha ya sha alwashin sasantawa da Eritrea
2018-04-03 09:57:22 cri
Sabon firaiministan kasar Habasha Abiy Ahmed ya jaddada aniyar kasar Habashan wajen dinke barakar dake tsakanin kasar da makwabciyarta Eritrea.

Ahmed, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a gaban majalisar wakilan kasar, inda ya sake mika goron gayyatar gwamnatin Eritrea domin neman amincewarta don shiga tattaunawar sulhu da nufin samun fahimtar juna da warware sabanin dake tsakanin bangarorin biyu.

Eritrea, wadda bangare ne daga cikin tarayyar kasar Habasha gabanin ta samu 'yancin kai a matsayin kasa a shekarar 1993, tana fuskantar zaman tankiya tsakaninta da Habasha musamman game rikicin kan iyakoki, lamarin da ya haddasa yaki tsakanin kasashe biyu daga shekarar 1998 zuwa 2000, wanda yayi sanadiyyar rayukan mutane 70,000 daga dukkan sassan biyu.

Sai dai gwamnatin kasar Habasha ta sha dora alhakin matsalar kan Eritrea, inda take zarginta da hannu wajen daukar nauyin kungiyoyin 'yan tada kayar baya, yayin da a nata bangaren, gwamnatin Eritrea tana zargin gwamnatin Habasha da hannu wajen daukar nauyin kungiyoyin 'yan tawayen na Eritrean tare da ruruta wutar fafutukar kafa kasar 'yan aware ta Red Sea.

Ahmed ya nanata aniyar Habasha wajen yin aiki tukuru domin lalibo hanyoyin tabbatar da zaman lafiya a kan iyakokin kasar har ma da wajen kasar baki daya.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China