Babban sakataren taron mista Zhou Wenzhong ya ba da jawabi a yayin taron manema labaru da aka shirya game da rufe taron, inda ya ce an shirya taron ne a yanayin da ake ciki na fuskantar kalubale a fannonin dunkulewar tattalin arzikin duniya da 'yancin cinikayya, da kuma rashin tabbaci kan makoma a nan gaba. Kusoshin da suka fito daga sassan siyasa, cinikayya, ilmi da kuma kafofin watsa labaru na kasashen Asiya da na duk duniya baki daya, sun taru don tattaunawa kan sabbin manufofi da hanyoyi da tsare-tsare, game da dunkulewar tattalin arzikin duniya, kana sun ba da shawarwari da shirye-shirye, kan cimma burin da aka sanya gaba yadda ya kamata. (Bilkisu)