in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin kasashe mahalarta dandalin Boao sun girmama tsarin bude kofa da Sin ke aiwatarwa
2018-04-11 10:37:39 cri

Shugabannin kasashe daban-daban mahalarta dandalin shekara-shekara na Boao na nahiyar Asiya, sun ce jerin matakan da Sin take dauka na habaka bude kofa ga kasashen waje, sun sami karbuwa sosai, kuma Sin za ta ba da gudunmawa ga ci gaban tattalin arziki duniya bisa nacewa wannan hanya.

Shugabannin sun bayyana haka ne a jiya Talata, yayin da aka bude dandalin shekara-shekara na Boao, a lardin Hainan dake kudancin kasar Sin, inda shugaban kasar Xi Jinping ya gabatar da jawabi.

Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya ce, a bana ne ake cika shekaru 40 da Sin ta fara gudanar da tsarin bude kofa ga kasashen waje, kuma suna ganin yadda Sin da duniya suke samun sauyi. Ya ce dandalin da aka yi a wannan karo, ya bayyana kuzari da karfin samun ci gaban nahiyar Asiya, kuma ya bayyana kokarin da ake yi na kafa al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama.

Shugaban Austria Alexander Van der Bellen ya ce, Mista Xi ya bayyana niyyar kasar Sin ta nacewa ga tsarin bude kofa da yin kwaskwarima a cikin jawabinsa, abun da ya ce zai amfanawa Sin, har ma da duniya baki daya.

A nata bangaren, shugabar asusun ba da laminu na duniya IMF Madam Christine Lagarde ta ce, Mista Xi ya ba da shawarar gudanar da tunanin kikire-kirkire da mutunta juna da bude kofa da dai sauransu a cikin jawabinsa, tare kuma da gabatar da tsare-tsaren bude kofa a dukkan fannoni, ciki hadda hada-hadar kudi da inshore da motoci da dai sauransu, tana mai cewa, ya kamata kasashe daban-daban su mayar da martani ta hanyar daukar matakan da suka dace bisa matsayin bai daya. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China