in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen duniya sun lura da jawabin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi a bikin bude taron dandalin tattaunawa na Asiya na Boao
2018-04-11 11:22:12 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci bikin bude taron shekara-shekara na dandalin tattaunawa na Asiya na Boao na bana, inda ya gabatar wani jawabi. Kasashen duniya sun kuma lura sosai da jawabin nasa, tare da yabawa manufar kasar Sin ta bude kofa ga kasashen waje da yin kwaskwarima.

Rahoton Jaridar The Wall Street Journal ta kasar Amurka ya ruwaito cewa, shugaba Xi Jinping ya yi alkawarin kara bada izini ga shiga kasuwa a fannin hada-hadar kudi da kere-kere, wanda ke nuna cewa Sin ta tabbatar da tsarin yin ciniki cikin 'yanci.

Shi ma Malami a fannin nazarin ilmin tattalin arizkin duniya na jami'ar Nairobi ta kasar Kenya Garrishon Ikiara ya ce, kamar yadda shugaba Xi ya bayyana, shawarar "ziri daya da hanya daya" ta bullo ne daga kasar Sin, amma dukkan duniya za su samu dama da moriya daga cikinta. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China