in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi: Kasashen da suka amince da tsarin ci gaba na bai daya a duniya za su cimma nasara
2018-04-11 09:54:49 cri

Mamba a majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya gabatar da jawabi yayin da ya halarci taron tsoffi da sabbin mambobin kwamitin dandalin Boao na shekara-shekara da aka yi jiya Talata, mai taken "Mutuntawa da dorawa kan manufofin dandalin Boao".

A cikin jawabinsa, Mista Wang a madadin kasa mai masaukin dandalin, ya bayyana godiya ga gudunmawar da mambobin kwamitin da masu ba da shawara suka bayar a cikin shekaru 8 da suka gabata, yana fatan sabon kwamiti zai dora a kan babbar manufar Boao wato "Yin hangen nesa da yin takara tare", don mayar da dandalin matsayin koli a duniya.

Ban da wannan kuma, Wang Yi ya ce, shugaba Xi Jinping ya gabatar da muhimmin jawabi da safiyar wannan rana, kuma ya yi imanin, dukkan kasashen duniya sun samu bayanai masu amfani daga jawabin.

Ya ce, ba shakka dandalin zai cimma nasara, saboda Sin za ta cimma nasara, haka zalika nahiyar Asiya, yana mai cewa, nasara na tare da duk wata kasa da ta amince da tsarin ci gaba na bai daya a duniya. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China