in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ababen jami'in kasar Sin ya shawarci nahiyar Afrika ta lalubo hanyoyin samar da ababen hawa marasa gurbata muhalli
2018-03-17 11:44:11 cri
Wani jami'in kasar Sin ya shawarci gwamnatocin Afrika su lalubo hanyoyin samar da kudi ga dabarun saamr da ababen hawa marasa gurbata muhalli.

Shugaban sashen ayyuka na cibiyar takaita fitar da hayaki mai gurbata muhalli daga ababen hawa na ma'aikatar kare muhalli ta kasar Sin Ma Dong, ya ce nahiyar a yanzu, na da hanyoyi da dama na samun kudi da damarmakin hadin gwiwa wajen samar da ababen hawa marasa gurbata muhalli a birane.

Yayin taro kan amfani da ababen hawa marasa gurbata muhalli da aka kammala jiya a birnin Nairobin kasar Kenya, Ma Dong ya ce Afrika na da damar amfana daga kawancen kasashe masu tasowa dake tsakanin nahiyar da kasar Sin. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China