in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Putin na Rasha zai kawo ziyara kasar Sin a watan Yuni
2018-04-06 12:15:43 cri
Kasashen Sin da Rasha sun amince su inganta dangantakar dake tsakaninsu, a lokacin da shugaban Rasha Vladimir Putin ya gana da Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi dake ziyara a kasar a jiya Alhamis, inda kuma Putin ya amince da gayyatar da kasar Sin ta yi masa na kawo mata ziyara a watan Yuni.

Wang Yi, ya kuma mika sakon taya murna da Shugaba Xi ya aike wa Shugaba Putin bisa sake lashe zaben shugaban kasar.

Ya ce ya kamata kasashen 2 su kara zurafafa matakin tuntunba da hadin kai tsakaninsu domin kara kare muradu da kasashensu, tare da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankunansu da ma duniya baki daya.

A nasa bangaren, Vladimir Putin ya bukaci Wang Yi ya isar da skonsa na taya murna ga Shugaba Xi Jinping, bisa zabarsa da daukacin majalisun kasar suka yi, da kuma nasarar kammala tarukan majalisun. Yana mai cewa sakamakon da aka cimma yayin tarukan zai kara yin tasiri ga makoma da ci gaban kasar Sin.

Da yake yabawa kyakkyawar dangantakar dake tsakanin ksashen biyu, Putin ya ce a matsayinsu na makwabta kuma abokan hulda, kasashen 2 sun kulla muhimmiyar dangantaka bisa kulawa da muradun juna ba tare da tsaurara matakai ba. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China