in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rasha: za a kori jami'an diplomasiyyar kasar Amurka 60
2018-03-30 10:10:49 cri
Maitaimakin Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Rybakov, ya kira jakadan Amurka dake kasar Jon Huntsman a jiya, don shaida masa matakin Rashar na korar jami'an diplomasiyyar Amurka 60 daga kasar, gami da rufe karamin ofishin jakadancin Amurka dake birnin St. Petersburg na Rasha.

Wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta fitar jiya, ta ruwaito cewa, Rasha ta dauki wannan mataki ne domin mayar da martani ga Amurka kan yadda ta kori wasu jami'an diplomasiyyarta.

Haka zalika, rahotanni na cewa, Rasha za ta soke takardar izinin da ta ba Amurka kan bude karamin ofishin jakadanci a St. Petersburg gami da gudanar da ayyuka a ciki, inda aka bukaci ma'aikatan kasar Amurka dake aiki a cikin karamin ofishin jakadancin su janye kafin ranar 31 ga watan Maris da muke ciki.

Rasha ta kara da cewa, Amurka ta dade tana tunzura mutane domin su nuna adawa gare ta, kuma la'akari da hakan ne ya sa ta ke fatan ganin Amurka ta nuna sanin ya kamata tare da dakatar da ayyukan da za su lahanta huldar dake tsakanin kasashen 2. Har ila yau, Sanarwar ta ce idan Amurka ta ci gaba da daukar matakan adawa kan jami'an diplomasiyyar Rasha dake kasarta, to ita ma Rasha za ta yi ramuwar gayya kan jami'an Amurka dake kasarta.

Ban da wannan kuma, yayin da Sergei Lavrov ministan harkokin wajen Rasha ke ganawa da wani jami'in MDD mai kula da batun Syria a jiya, Lavrov ya ce, Rasha za ta mayar da martani makamancin wanda ta dauka kan Amurka, kan kasashen da suka bi sahun Amurkar na korar jami'an diplomasiyyar kasarsa. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China