in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Minista: Sin a shirye take ta yi hadin gwiwa don tabbatar da tsaron kasa da kasa
2018-04-05 13:04:23 cri
Ministan tsaron kasar Sin janar Wei Fenghe, ya ce kasarsa a shirye take ta kyautata hadin gwiwa da sauran kasashen duniya don tabbatar da tsaron kasa da kasa da kafa wani tsari na cin moriyar juna da samar da kyakkyawan yanayi mai cike da tsaro a duniya baki daya.

Kasar Sin a shirye take ta yi aiki da sauran kasashen duniya wajen daukaka matsayin duk wani mataki da zai tabbatar da tsaro, da kuma warware dukkan sabani ta hanyar lumana, janar Wei ya fadi hakan ne a lokacin taron karawa juna sani na kasa da kasa kan sha'anin tsaro a Moscow karo na 7.

Ya ce, samar da zaman lafiya da ci gaba batutuwa ne da ba za'a iya yin watsi da su ba a wannan zamanin, kuma batutuwa ne da suka shafi duniya baki daya. Ya kara da cewa, tunanin yin hadin gwiwa da cin moriyar juna yanayi ne dake samun karbuwa a duk duniya, mutunta juna da amincewar juna su ne matakan da za'a yi amfani da su wajen tafiyar da harkokin kasa da kasa.

Janar Wei ya ce, a lokacin babban taron jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 19 wanda ya gudana a watan Oktoban shekarar 2017, da kuma manyan taruka biyu na kasar da aka gudanar a cikin wannan shekarar, shugaba Xi Jinping ya nanata aniyar kasar Sin na nacewa kan matsayinta na tabbatar da zaman lafiya da gina ci gaba, don samar da kyakkyawar makoma ga bil adama.

Ministan tsaron na kasar Sin ya kara da cewa, kasarsa a shirye take ta bada gudummawa wajen samar da zaman lafiyar duniya, da kuma ingiza cigaban kasa da kasa da mutunta dokokin kasa da kasa. (Ahamd FAgam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China