in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta bayyana korar jami'an diflomasiyyarta da Rasha ta yi a matsayin abun takaici da bai dace ba
2018-03-30 13:29:39 cri
Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta wallafa a shafinta na Twitter cewa, matakin Rasha na korar jami'an diflomasiyyar kasar 60 abun takaicin ne da bai dace ba.

Ta kara da cewa, Rashar na kara ware kanta, bisa matakin da ta dauka na korar Jami'an, bayan sanyawa tsohon jami'in liken asirinta da 'yarsa guba a Birtaniya.

Kakakin ma'aikatar Heather Nauert, ya ce kasashe 28 ne suka bi sahun Amurka na korar jami'an Rasha 153 daga kasashensu.

A farkon wannan makon ne Amurka ta kori jami'an diflomasiyar Rasha, a wani mataki na mayar da martani ga harin guba da aka kai wa tsohon jami'in leken asiri Rasha da 'yarsa a birnin Salisbury dake kudu maso yammacin Birtaniya a ranar 4 ga wannan watan.

Da yake martani, Jakadan Rasha a Amurka Anatoly Antonov, ya bayyana a ranar Litinin da ta gabata cewa, Moscow za ta dauki mataki daidai da wanda aka dauka kanta cikin 'yan kwanaki.

Daga bisani ne kuma ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta bayyana korar jami'anta da kasashen yamma suka yi a matsayin adawa da ita, inda ta lashi takobin mayar da martani. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China