Wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar a jiya, ta ce wannan martani ne da Rasha ta mayar ga wadannan kasashen da suka kori jami'an diplomasiyyarta.
Rasha ta bayyana cewa, bisa zarginta da Birtaniya ta yi na sanyawa tsohon jami'inta na leken asirin Sergey Skripal da 'yarsa guba ba tare da tushe ba, kasashen 23 suka tsaida kudurin korar jami'an diplomasiyyarta, a don haka, ita ma za ta kori jami'an diplomasiyyarsu da yawansu ya yi daidai da na jami'anta da suka kora.
Ban da wannan kuma, ma'aikatar harkokin wajen Rashar ta gabatar da sanarwa ta daban a wannan rana, inda ta ce ta kira jakadan Birtaniya dake kasar, don nuna rashin jin dadinta game da matakin Birtaniya na sa kaimi wajen ganin sauran kasashe sun kori jami'an diplomasiyyarta. (Zainab)