Kasashe 5 da suka hada da Burkina Faso da Chadi da Mali da Mauritania da Niger ne suka kafa rundunar G5 a shekarar 2014, da nufin inganta hadin kai a yankin da kuma magance kalubale na bai daya da suke fuskanta.
A gefen taron AU kan yankin ciniki cikin yanci na nahiyar Afrika ranar Alhamis da ta gabata a birnin Kigali, shugaban Rwanda Paul Kagame ya sanar da bayar da gudunmuwar dala miliyan 1 domin tallafawa ayyukan rundunar.
Cikin wata sanarwa da aka fitar a jiya Juma'a, Paul Kagame ya lashi takobin kasar za ta ci gaba bada goyon baya ga rundunar.
Da yake yabawa kokarin Rwanda ga rundunar, Shugaban hukumar AU Moussa Faki Mahamat, ya ce gudunmuwar ta bayyana irin karfin hadin kai dake tsakanin kasashen dangane da yaki da ta'addanci da sauran laifuka.
Har ila yau, Moussa Faki Mahamat ya roki kasashe mambobin AU su mara baya ga kasashen kungiyar G5. (Fa'iza Mustapha)