in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nasarorin da matasa uku suka cimma a sabon yankin Xiong'an
2018-04-02 13:01:46 cri

A ranar 1 ga watan Aflilun shekarar 2017, kasar Sin ta tsaida kudurin kafa sabon yankin Xiong'an na lardin Hebei. A wannan lokacin da aka cimma shekara guda da kafa yankin, wakilanmu sun zanta da matasa uku dake sana'a a yankin, don sauraren burinsu na raya sana'a. Wadannan matasa uku, sun hada da wani 'dan asalin yankin Xiong'an da wani da ya dawo kasar Sin bayan digirin digir-gir, yayin da dayan manomi ne dan ci rani.

Hanyar Aowei dake gundumar Rongcheng ta sabon yankin Xiong'an a yanzu haka ta kasance wani titin kamfanoni, titin hanya ce dake a zagaye, inda ta saka gundumar a tsakiya. A cikin wadannan kamfanoni da dama dake kan titin, akwai wani karamin kamfanin ba da shawara da Xiao Gang da abokansa uku suka kafa.

Game da burinsu na kafa kamfanin, Xiao Gang ya ce, a yammacin ranar 1 ga watan Aflilun bara, ya samu labarin kafa sabon yankin Xiong'an ta rediyo a yayin da yake tukin mota, sai ya tsaida motarsa a gefen hanya na tsawon lokaci, bayan tunani sosai da ya yi, sai ya bugawa abokansa waya, don su tattauna sosai a kai. A cewar Xiao Gang, yawancin mutanen da suka zo nan Xiong'an sun zo ne domin neman sabuwar damar samun ci gaba.

Ga wadancan kamfanoni da dama dake bulluwa a titunan Xiong'an cikin sauri, Xiao Gang da abokansa sun gano cewa, 'yan kasuwar sun zo Xiong'an ne don gudanar da cinikayya daga wasu wurare, kuma ba shakka suna bukatar hidima a fannonin samun shawarari da neman ma'aikata da dai sauransu. Al'amarin da ya sa suka yanke shawarar kafa kamfanin ba da shawara, don ba da hidimar samar da ma'aikata da ta tsabtar muhalli da sauransu.

"Sabon yankin nan wani babban dandamali ne, hakan ya samar da babbar damar ci gaba, bisa wannan yanayin da ake ciki, muna son neman ci gaba a nan, amma ba bisa tsohuwar hanya ba. Game da ni kai na, ina son gano kwarewata bisa ci gaban sabon yankin. Wannan ma shi ne burin abokai na a matakin farko."

Sabon yankin Xiong'an dake birnin Baoding na lardin Hebei na kasar Sin, ya shafi gundumomi uku, ciki har da Xiongxian, Rongcheng da Anxin, da kuma wasu yankunan dake kewayensu. Yankin ya kasance wani muhimmin wuri dake tsakanin biranen Beijing, da Tianjin da kuma Baoding. Tsohuwar hanya da Xiao Gang ya ambata a baya tana nufin wasu sana'o'in gargajiya da wadannan gundumomin uku na sabon yankin Xiong'an suka yi a da, kamar su fitar da tufaffi, da takalma, da kuma roba da dai sauransu. Matsayin da kasar Sin ta tabbatar kan ci gaba da yin kirkire-kirkire a sabon yankin Xiong'an ya sanya wasu matasa ciki har da Xiao Gang tabbatar da sabon burin su. Xiao Gang ya ce, ciniki na farko da kamfaninsu ya yi shi ne samar da hidimar tsabtar dakunan kwana ga wani kamfani, inda suka samu kudin shiga na yuan 150. Amma, ya na fatan kamfaninsu ma zai bi hanyar samun ci gaba ta fuskar kimiyya da fasahar zamani cikin sauri, ya ce,

"Dukkanmu ba mu yi karatu mai yawa ba, muna bukatar koyon Karin ilmi game da yin nazari ta hanyar tattara bayanai a fannoni da dama (big data). Gaskiya abubuwan da muke da bukatar koyo suna da yawa, za mu yi kokarin samu ci gaba a fannin."

Kafuwar sabon yankin Xiong'an ba kara kwarin gwiwa ga matasan wurin kamar Xiao Gang da abokansa kadai ya yi ba, har ma da jan hankulan wasu matasa da suka samu digirin karatu a kasashen ketare, ciki har da Yang Jingzhou, wani masanin kimiyya da fasaha. Yang Jingzhou ya ce, burinsa shi ne taimakawa yankin Xiong'an wajen yin gyare-gyare kan sana'o'in gargajiya ta hanyar fasahar gurza ta 3D. Ya bayyana cewa,

"A gani na, irin fasahar ta fi samun karbuwa a wajen masu masana'antu da fitattun matasa dake aiki a wurin, don tabbatar da samun sauyawar sana'o'insu."

A watan Disamban bara, Wang Jinhui da wasu manoma 'yan cin rani sama da 100 suka iso nan Xing'an don kafa cibiyar ba da hidima ga mazauna Xiong'an. Wang Jinhui ya ce, sabon tsarin da Xiong'an ya samar ga mutanen da suka zo wurin aiki daga sauran yankuna, abun da ya sa yake cike da imani kan makomarsa, ya ce,

"Muna son irin tsari, don ya taimaka wajen warware matsalar samun gurbin karatu da 'yayanmu ke fuskanta." (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China