in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Fasinjoji kusan dubu 500 sun ji dadin zirga-zirga ta jiragen kasa masu saurin tafiya tsakanin Beijing da Xiong'an
2018-04-01 14:14:41 cri

Yau rana ce ta cika shekara 1 da kafuwar yankin Xiong'an na lardin Hebei. Tun daga watan Yulin bara, jiragen kasa masu saurin tafiya 2 sun fara zirga-zirga wadanda suka tashi daga birnin Beijing, inda kuma suka wuce yankin Xiong'an zuwa birnin Baoding na lardin Hebei. Sakamakon haka, fasinsojin dake tafiye-tafiye tsakanin Beijing da yankin Xiong'an domin kai ziyara ga iyalansu ko yin aiki ko yin kasuwanci ko shan iska sun samu saukin tafiya kamar yadda suke fata. Ya zuwa ran 30 ga watan Maris da ya gabata, yawan fasinjojin da suka yi amfani da wadannan jiragen kasa masu saurin tafiya ya kai kimanin dubu 487.8, daga cikinsu, yawan fasinjojin da suka tashi ko suka sauka a tashar Baigou da ta tafkin Baiyangdian wadanda suke yankin Xiong'an ya kai dubu 148.8, wato ya kai kashi 30 cikin dari bisa na jimillar fasinjojin da aka yi jigilarsu. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China