in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Muna taya murnar cika shekara guda da kafuwar sabon yankin Xiong'an a Sin
2018-04-01 15:30:50 cri
A ranar 1 ga watan Afrilu na shekarar 2017 da ta wuce, kwamitin tsakiya na JSK da majalisar gudanarwar kasar ta Sin suka fidda sanarwa cewa, an tsai da kudurin kafa sabon yankin Xiong'an a lardin Hebei na kasar Sin, wanda ya kasance yankin musamman da aka kafa bayan kasar Sin ta shiga sabon zamani na yin kwaskwarima da bude kofa ga waje. Ya kasance wani babban kuduri ne da kwamitin tsakiya na JKS dake karkashin jagorancin shugaba Xi Jinping ya yi, bayan kafuwar yankin musamman na tattalin arziki na birnin Shenzhen da sabon yankin Pudong na birnin Shanghai, wanda zai bada tabbaci ga kasar Sin wajen neman dawaumammen ci gaba.

A yau kuma, an cika shekara daya da kafuwar sabon yankin Xiong'an a nan kasar Sin.

Xiong'an shine zai zama wani sabon birni, inda aka tattara karfi daga bangarori daban daban na kasar Sin wajen yin kwaskwarima da bude kofa ga waje cikin sabon zamani. Haka kuma, ci gaba na wannan birni zai nuna farfadowar kasar Sin baki daya da kuma babbar bunkasuwar kasa da kasa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China