in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabon yankin Xiong'an zai samar da fasahohi ga bunkasuwar yankunan kasar Sin a nan gaba
2018-04-02 11:08:31 cri
Ranar 1 ga watan Afrilu aka cika shekara guda da kafa sabon yankin Xiong'an, inda aka samu babban ci gaba a fannonin gina ayyukan more rayuwa, da samar da aikin yi da sauransu. Shugaban kwalejin nazarin kwaskwarima da ci gaba na kasar Sin dake lardin Hainan Chi Fulin ya bayyana cewa, kafuwar yankin ta bude sabon shafin samun bunkasuwa tare a yankunan Beijing, Tianjin da Hebei.

Mr Chi ya bayyana cewa, wannan mafari ne da ya kasance daga tsara tsare-tsare zuwa aiwatar da tsare-tsaren a dukkan fannoni. A ganinsa, a shekarar 2018, za a kafa sabon tsarin samun bunkasuwa tare a yankin Beijing, Tianjin da Hebei bisa aikin sa kaimi ga raya yankin Xiong'an. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China