in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin Sin ya jaddada muhimmancin tabbatar da zaman lafiya a Kongo Kinshasa
2017-08-19 13:10:40 cri
Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin dake MDD mista Wu Haitao, ya jaddada cewa, yana da muhimmanci a tabbatar da zaman karko a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, kana ya yi kira ga kasashen dake shiyyar da sauran kasashen duniya, su nuna goyon baya ga yunkurin tabbatar da zaman lafiya a kasar.

Mista Wu Haitao, ya bayyana haka ne a yayin da yake jawwabi a wajen taron bude kofa na kwamitin sulhun MDD game da batun saka takunkumi ga Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo.

A cewarsa, kasar Sin na yabawa kokarin da sabuwar gwamnatin wucin gadin ta kasar ke yi wajen karfafa kiyaye tsaro da gudanar da harkokin kasa.

Ya kuma yabawa muhimmiyar rawar da wasu kungiyoyin nahiyar ciki har da kungiyar AU da kasashe makwabta suke takawa kan warware matsalar kasar,

Mista Wu ya kuma bayyana cewa, ya kamata kwamitin sulhu na MDD ya kara daidaita hadin kan kasashen duniya, inda ya jaddada cewa, abin da ya fi muhimmanci kasashen duniya su sa a gaba shi ne, kalubalantar bangarori daban-daban na kasar Kongo Kinshasa, musamman ma masu adawa da gwamnati, don su tsagaita bude wuta da dakatar da rikici da nuna karfin tuwo ba tare da bata lokaci ba.

A cewarsa, a yayin da kasashen duniya ke taimakawa kasar, kamata ya yi su girmama jagorancin gwamnatin kasar da zaben jama'ar kasar, domin sai da hakan ne za a iya cimma kyakyawan sakamako.

Baya ga haka, mista Wu ya ce, kwamitin sulhu ya dauki matakai da dama na murkushe ayyukan da suka sabawa doka da wasu bata gari ke yi, kuma an samu nasarori a wannan fannin.

Sai dai kuma, kamata ya yi a gane cewa, saka takunkumi ba buri ne da ake son cimmawa ba, hanya ce kawai da ake bi don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.

Bugu da kari, Mista Wu ya ce, ko da yaushe gwamnatin kasar Sin na goyon bayan yunkurin zaman lafiyar Kongo Kinshasa, tana kuma bada tallafi wajen gina kasar, inda ya ce Kasar Sin na fatan yin kokari tare da sauran kasashen duniya, wajen kara taka muhimmiyar rawa don ganin an tabbatar da zaman lafiya da raya kasar. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China