Rahotanni sun ce, tun daga daren ranar Laraba, aka fara mamakon ruwan sama a yankin tabkin Albert dake lardin Ituri na kasar, lamarin da ya haddasa bala'in zaizayar kasa kashegari.
A nashi bangare, Pacifique Keta, mataimakin babban Gwamnan lardin Ituri, ya fadawa manema labarai cewa, zuwa yanzu kasa da laka sun binne a kalla gidajen iyalai 50 a wasu kauyuka 3, sa'an nan yawan mutanen da suka rasa rayukansu ya karu zuwa tsakanin 150 zuwa 200.
A cewar jami'in, gwamnatin kasar ta riga ta tura karin kungiyar aikin ceto zuwa wurin da bala'in ya abku don kai dauki.
Tabkin Albert ya kasance cikin yankin babban tabki dake gabashin Afirka, inda yake kan iyakar dake tsakanin jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo da kasar Uganda. Sannan ya kasance tabki mafi girma na 7 a nahiyar Afirka. Ana samun ruwan sama sosai a wuraren dake dab da tabkin, lamarin da kan haddasa bala'in zaizayar kasa.(Bello Wang)