in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ba ta son yakin cinikayya, amma komai ba ta tsoronsa
2018-03-27 10:03:56 cri

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Zheng Zeguang, ya ce dangantakar tattalin arziki da cinikayya dake tsakanin kasar Sin da Amurka ta moriyar juna ce, kuma ta samar da muhimman alfanu ga kasashen.

Da yake jawabi ga taro kan ci gaban kasar Sin jiya Litinin a nan birnin Beijing, Zheng Zeguang, ya ce kasar Sin ba ta son yakin cinikayya, amma komai ba ta taba jin tsoronsa ba. Inda ya ce, kasar ta shirya tsaf don tunkarar irin wannan yanayi da nufin kare muradunta.

Ya kuma bayyana fatan cewa, Amurka za ta sassauta tare da samar da mafita.

A ranar Alhamis din da ta gabata ne shugaban Amurka Donald Trump ya rattaba hannu kan wata takarda da za ta kakaba harajin da ya kai dala biliyan 60 kan kayayyakin da kasar Sin ke shigarwa kasar tare da takaita jarin da Sin din za ta zuba a Amurka. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China