in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan sandan Sin sun mayar da wani mai aikata laifi ga Amurka
2017-10-16 15:46:50 cri

A yau Litinin ne 'yan sandan kasar Sin suka mika wa takwarorinsu na Amurka, wani BaAmurken da ake zargi da aikata laifi, sannan ya tsere daga kasarsa zuwa nan kasar Sin, a filin jiragen sama na Pudong dake birnin Shanghai na kasar Sin bisa bukatar hukumar shari'a ta Amurka, 'yan sandan Amurka za su tasa keyarsa zuwa kasarsu. Wannan shi ne sabon sakamakon da aka samu tun bayan da kasashen Sin da Amurka suka fara gudanar da hadin gwiwa a fannin shari'a a ranar 4 ga watan nan da muke ciki.

Rahotanni sun ce, ana zargin BaAmurken da yi wa yara masu shekaru tsakanin 6 zuwa 12 fyade sau da dama tsakanin watan Yulin shekarar 2009 zuwa Agustan 2012.

A watan Yunin shekarar 2016 ne aka shedawa 'yan sanda laifinsa, inda nan take suka fara gudanar da bincike kan lamarin, sai da wanda ake zargin ya gudu ya bar waje.

A watan Yunin bana ne hukumar 'yan sandan kasa da da kasa ta bayar da sanarwar kama shi a duk inda yake a fadin duniya.

Bayan binciken da aka yi, an gano cewa, mutumin ya iso birnin Shanghai na kasar Sin a watan Mayun bana, al'amarin da ya sa hukumar 'yan sandan Amurka gabatar da bukatar hukumar 'yan sandan kasar Sin ta taimaka mata, inda daga bisani 'yan sandan na kasar Sin suka yi nasarar cafke shi.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China