in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin: Yadda jirgin ruwan Amurka ya ratsa tsibirin Xisha wata takala ce
2017-07-03 09:52:34 cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya bayyana cewa, yadda jirgin ruwan Amurka mai kakkabo makamai masu linzami ya ratsa yankin ruwayen dake gabar tsibirin Xinsha na kasar Sin, tamkar takala ce ta fannin siyasa da kuma harkar soja.

Lu Kang wanda ya bayyana hakan a jiya cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, ya ce yanzu haka kasar Sin ta tura jiragen ruwa na soja da jiragen saman yaki don isar da sakon gargadi ga jirgin ruwan na Amurka.

A jiya ne dai jirgin ruwan kasar ta Amurka mai kakkabo makamai masu linzami mai suns USS Stethem, ya ratsa yankin ruwayen kasar Sin dake gabar tsibiran Xisha.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China