in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta jaddada kudurin tabbatar da zaman lafiya a zirin Koriya
2016-01-08 09:38:32 cri

Kasar Sin ta sake jaddada matsayinta na kawar da makaman nukiliya da kuma tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a zirin Koriya.

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ne ya bayyana hakan yayin tattaunawarsa ta wayar tarho da takwaransa na kasar Amurka John Kerry dangane da halin da ake ciki a zirin na Koriya.

Mr Wang ya ce, kasar Sin tana son tattaunawa da dukkan bangarorin da lamarin ya shafa, ciki har da kasar Amurka.

A nasa jawabin, sakatare Kerry ya bayyana matsayin kasar ta Amurka game da gwajin makamin nukiliya na baya-bayan nan da kasar Koriya ta Arewa ta yi. Yana mai cewa, Amurka tana fatan ci gaba da tattaunawa da kasar Sin game da halin da ake ciki a zirin na Koriya.

Jami'an kasashen biyu sun kuma tattauna game da batun nukiliyar Iran da kuma dangantakar da ke tsakanin Sin da Amurka.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China