in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Amurka za su karfafa yin musaya da hadin gwiwa a tsakaninsu
2017-03-01 09:48:19 cri

Kasashen Sin da Amurka sun bayyana kudurinsu na karfafa yin shawarwari da yin musaya a dukkan matakai, da nufin fadada hadin gwiwa kan harkokin duniya da shiya-shiyya.

Bangarorin biyu sun jaddada wannan mataki ne yayin wata ganawa tsakanin sakataren harkokin kasashen wajen Amurka Rex Tillerson da mamba a majalisar gudanarwar kasar Sin Yang Jiechi wanda a halin yanzu ke ziyara a kasar ta Amurka.

Yang ya ce, muddin kasashen biyu suka martaba ka'idojin rashin takalar juna da yin fito-na fito da matuntu juna da cin moriyar juna, to kasar Sin a shirye ta ke ta hada kai da Amurka a mataki na gaba, da kara bunkasa yin musaya a tsakaninsu a dukkan fannoni.

Sauran sun hada da zurfafa yin shawarwari da kulla hadin gwiwa daga dukkan fannoni da zurfafa sadarwa da tsara batutuwan da suka shafi harkokin kasa da kasa da na shiyya-shiyya, da mutunta muradun juna kan muhimman batutuwa.

A nasa jawabin, sakatare Tillerson ya ce, ita ma Amurkar a shirya ta ke ta yi aiki da kasar Sin, ta yadda bangarorin biyu za su kara fadada hadin gwiwar da ke tsakaninsu, da zurfafa yin shawarwari da musaya tsakanin manyan jami'an kasashen biyu. Sauran sun hada da ci gaba da fadada hadin gwiwa a dukkan sassa, da yin taka-tsantsan kan batutuwa masu sarkakiya ta hanyar yin shawarwari da gudanar da tsare-tsare.( Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China