in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An samu raguwar yaduwar cutar Lassa a Nijeriya
2018-03-27 09:51:11 cri

Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta ce bayan tabbatar da mutane 400 sun kamu da zazzabin Lassa yayin da wasu 100 suka mutu sanadin ta, a yanzu an fara samun raguwar yaduwarta, sai dai har yanzu da sauran rina a kaba.

Kididdiga daga hukumar WHO da cibiyar takaita yaduwar cutuka ta Nijeriya NCDC, sun nuna cewa, adadin sabbin masu kamuwa da cutar da wadanda ake hasashen sun kamu da ita ya ragu cikin makonni 5 a jere, sai dai ana sa ran za a samu karin kamuwa da ita daga nan har zuwa karshen lokacin rani, la'akari da yadda zazzabin ya fi kamari a yankin.

Kawo yanzu a bana, rahoton hukumar NCDC ya ce, gwaje-gwaje da aka yi sun tabbatar da mutane 394 sun kamu da cutar, inda mutane 18 ne suka kamu da ita cikin makon da ya gabata, adadin da ya ragu idan aka kwatanta da mutane 54 aka samu a watan da ya gabata.

A cewar wakilin WHO a Nijeriya, Dr. Wondimagegnehu Alemu, ya kamata a yi taka tsantsan wajen bayyana raguwar adadin, inda ya ce, har yanzu cutar ta Lassa ba ta kawo karshe ba. A don haka ya ce, akwai bukatar a ci gaba da sanya ido da gudanar da ayyukan tunkarar cutar, don tabbatar da ci gaba da cudanya da al'ummomi da nufin taimakawa wajen kare ci gaba da yaduwarta. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China