in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An sake samun bullar zazzabin Lassa a Nijeriya
2017-06-20 09:19:56 cri

Gwamnatin jihar Anambra dake kudu maso gabashin Nijeriya, ta tabbatar da sake bullar zazzabin Lassa, wanda dangin bera ke yada shi, bayan mutuwar wani dalibin dake nazarin fannin aikin likita a jihar.

Daraktan sashen kula da lafiyar al'umma na jihar Emmanuel Okafor, ya ce akwai kuma wasu mutane 65 da ake sanyawa ido, bayan sake samun bullar cutar.

Emmanuel Okafor ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, gwaje-gwajen da aka yi sun nuna cewa, mutane 2 daga cikin wadancan 65 din, sun riga sun kamu da zazzabin.

Ya kuma tabbatar da cewa, gwamnatin jihar na da dukkan abubuwan da ake bukata na takaita yaduwar cutar.

Barkewar zazzabin a Nijeriya cikin farkon shekarar da ta gabata, ta yi sanadin mutuwar mutane sama da 80. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China