in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya za ta yi bincike kan zazzabin Lassa
2016-01-20 10:01:00 cri

Gwamnatin Najeriya ta kafa wani kwamiti wanda zai bincika tare da daukar matakan dakile bullar annobar zazzabin Lassa wanda ta yi sanadiyyar lakume rayukan mutane 50 a kasar.

Kwamitin har ila yau, shi ne ke da alhakin gudanar da aiki kafada da kadafa tsakanin gwamnatin kasar da sauran hukumomi masu zaman kansu dake yaki da yaduwar cutuka.

Oyewale Tomori, farfesa a fannin nazarin yaduwar cutuka shi ne ke jagorantar kwamitin, dama dai ya taba gudanar da bincikin kan bullar cutar zazzabin Lassa tun a shekarar 1969.

Da yake kaddamar da kwamitin a Abuja, ministan lafiya na kasar Isaac Adewole, ya ce, gwamnatin kasar tana da kyakkyawan fatan kwamitin zai yi amfani da shawarwarin kwararru domin daukar dukkanin matakan dakile wannan annoba.

Haka zalika ana sa ran kwamitin zai gabatar da ingantaccen tsari na gudanar da rigakafin kamuwa daga cutar a asibitoci domin kawar da yaduwar cutar ta zazzabin Lassa daga kasar kwacokan.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
ga wasu
v Zazzabin Lassa ya halaka mutane 41 a Najeriya 2016-01-13 09:51:08
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China