in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta gano sabuwar cutar Lassa a jihar Plateau
2017-07-26 09:01:13 cri

A ranar Talata Najeriya ta bayyana cewa, an samu bullar cutar zazzabin Lassa a jihar Plateau, sai dai kuma ana ci gaba da hada karfi da karfe domin dakile bazuwar cutar a kasar.

Kuden Deyin, shi ne kwamishinan lafiya na jihar Plateau, ya bayyana cewa, an samu bullar zazzabin na Lassa guda hudu ne ta hanyar ta'ammali da halittu dangin beraye.

Daga cikin mutanen 4 da suka kamu da cutar, an tabbatar da mutuwar mutum guda, yayin da ragowar mutanen 3 suke samun kulawa a asibiti.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China