Gwamnan jihar Ondo dake kudancin Najeriya Oluwarotimi Akeredolu, ya ce sakamakon bincike a dakunan gwaji, ya tabbatar da kamuwar mutane 36 da zazzabin Lassa a jihar ta Ondo, ciki hadda mutane 9 da tuni suka riga mu gidan gaskiya.
Gwamna Akeredolu ya ce, gwamnatin sa ta kaddamar da shirin gaggawa na yaki da yaduwar cutar a mataki na jiha da na kananan hukumomi.
Cutar zazzabin Lassa dai ta barke ne a farkon watan Janairun da ya gabata kamar yadda mahukuntan kasar suka tabbatar.
A makon jiya, babban darakta mai kula da cibiyar yaki da cututtuka ta Najeriya Chikwe Ihekweazu, ya shaidawa taron manema labarai cewa, zazzabin na Lassa ya hallaka mutane 21 a Najeriya.
Cutar zazzabin Lassa dai wasu nau'in kwayoyin cuta ne dake iya yaduwa a kowane lokaci ko yanayi ke haifar da ita, ko da yake ta fi kamari a lokacin bazara. Ana kuma iya kandagarkin yaduwar ta ta hanyar kula da tsaftar muhalli, da kaucewa taba duk wani abu da bera ya taba, tare da tsaftace gida yadda ya kamata.(Saminu)