in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Amurka ya gana da wakilin majalisar gudanarwar Sin
2017-02-28 10:28:25 cri
A jiya Litinin ne shugaban kasar Amurka Donald Trump ya gana da wakilin majalisar gudanarwar kasar Sin Yang Jiechi a fadar White House ta kasar Amurka.

A yayin ganawar tasu, Yang Jiechi ya bayyana cewa, kasar Sin tana son karfafa cudanyar dake tsakanin shugabanni da al'ummomin kasashen biyu, bisa ka'idojin magance nuna adawa da juna, da girmamawa da kuma yin hadin gwiwa domin cimma moriyar juna. Bugu da kari, ya ce, habaka shawarwari da hadin gwiwar kasar Sin da kasar Amurka kan harkokin dake shafar kasashen biyu da ma kasa da kasa, da nuna fahimta kan muhimman muradun kasashen biyu da kuma harkokin da kasashen biyu suka fi mai da hankali, za su ba da gudummawa wajen inganta dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasar Amurka yadda ya kamata, kana zai ba da karin tallafi ga al'ummomin kasashen biyu, har ma ga al'ummomin kasa da kasa baki daya.

A nasa bangare, Mr. Trump ya ce, kasar Amurka tana mai da hankali sosai kan dangantakar hadin gwiwa dake tsakaninta da kasar Sin. Ya ce, ya kamata kasashen biyu su karfafa mu'amalar dake tsakanin shugabanninsu, da zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu bisa fannoni daban daban, da kuma kara yin shawarwari da hadin gwiwa a harkokin shiyya-shiyya da na kasa da kasa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China