in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya zanta da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron ta wayar tarho
2018-03-22 20:29:11 cri
Yau Alhamis shugaban kasar Sin Xi Jinping ya zanta da takwaransa na kasar Faransa Emmanuel Macron ta wayar tarho.

A yayin zantawar tasu, Mr. Macron ya taya Xi Jinping murnar sake cin zaben zama shugaban kasar Sin. Ya kuma bayyana cewa, yana dora muhimmanci kwarai kan zumuncin dake akwai tsakanin kasarsa da Sin, yana ma mayar da hankali sosai kan nasarori daban daban da aka cimma a gun taruka biyu na kasar Sin, wadanda aka rufe ba da dadewa ba, wato taron NPC da na CPPCC. Kana ya bayyana fatansa na karfafa hadin kai da cudanya a tsakanin kasashen biyu a fannoni daban daban.

A nasa bangaren Xi Jinping ya bayyana cewa, a nan gaba kasar Sin za ta ci gaba da zurfafa kwaskwarima da bude kofa ga ketare, yana da imanin cewa, bunkasuwar kasar Sin zai kara samar da damammaki masu kyau, ga hadin kai tsakanin Sin da Faransa da kuma Sin da Turai. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China