A yau Litinin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mika sako ga Emmanuel Macron don taya shi murnar zama sabon zababben shugaban kasar Faransa.
A cikin sakon, shugaba Xi ya nuna cewa, kasar Faransa kasa ce ta farko a yammacin duniya da ta kulla huldar diplomasiyya tare da kasar Sin. Dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu na da muhimmiyar ma'ana gare su har ma da duk duniya baki daya. A 'yan shekarun nan, ana raya dangantakar yadda ya kamata. Kasar Sin da kasar Faransa zaunannun mambobi ne na kwamitin sulhu na MDD, wadanda ke taka muhimmiyar rawa a duniya. An kuma dora musu babban nauyi wajen sa kaimi ga zaman lafiya da ci gaban duniya.
Shugaba Xi ya kara da cewa, ciyar da dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu zuwa gaba yadda ya kamata, ba kawai zai amfanawa kasashen biyu da jama'arsu ba ne, hatta ma zai taimaka wajen samun zaman lafiya da kwanciyar hankali da ma wadata a duk fadin duniya. Kasar Sin na son hadin gwiwa tare da Faransa don raya dangantakar abokantaka tsakaninsu daga dukkan fannoni bisa manyan tsare tsare har zuwa wani sabon mataki.(Kande Gao)