Lu ya bayyana haka ne a yayin taron manema labaru da aka yi yau Alhamis a nan birnin Beijing, inda ya kara da cewa, kasashen Sin da Faransa sun samu sakamako mai kyau a fannonin siyasa, tattalin arziki da cinikayya, al'adu da dai sauransu. Wannan ya nuna kyakkyawar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni, ta kuma aza harsashi mai kyau wajen bunkasa dangantakar dake tsakaninsu a sabon zamani.
Kwanan baya ne, shugaba Emmanuel Macron na kasar Fransa ya kammala ziyarar da ya ke a nan kasar Sin. (Bilkisu)