in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin raya Afirka yana sa ran ganin karuwar tattalin arzikin yammacin Afirka da kashi 3.8%
2018-03-22 11:26:10 cri
Bankin raya cigaban nahiyar Afirka AFDB ya gabatar da wani rahoto kan tattalin arzikin nahiyar a kwanakin baya, inda ake sa ran ganin karuwar tattalin arzikin yammacin Afirka da kashi 3.8% a shekarar nan ta 2018, haka kuma zuwa shekarar 2019 adadin zai iya kaiwa kashi 3.9%. Haka zalika, rahoton ya nuna yiwuwar samun karin farfadowar tattalin arzikin a sakamakon hauhawar farashin kayayyakin masarufi gami da wasu sinadarai.

A cewar rahoton, bayan shekaru masu yawa da ake ta kokarin raya yankin yammacin Afirka, karuwar tattalin arzikin yankin ya tsaya kan kashi 0.5% kawai a shekarar 2016. Kana manyan dalilan da suka haddasa wannan tsaiko sun hada da raguwar farashin wasu sinadarai, da kuma koma bayan tattalin arzikin kasar Najeriya, bisa la'akari da yadda karfin tattalin arzikin Najeriya ya kai kashi 70% na daukacin yankin.

Ban da haka kuma, wata jami'ar bankin AFDB mai kula da yankin yammacin Afirka ta ce, wani babban kalubalen da ake fuskanta a yankin shi ne na batun samar da guraben aikin yi ga matasa.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China