in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta ce tsoffin motoci ne ke kara fitar da abubuwan dake gurbata muhalli a Afirka
2018-03-16 09:25:31 cri
Shugaban sashen kula da ingancin iska da ababan hawa na shirin kare muhalli na MDD Rob de Jong ya ce galibin motoci masu amfani da man dizel da ake sayarwa kasashen nahiyar Afirka suna fitar da abubuwa masu gurbata muhalli da dole ne a mayar da hankali a kai.

Jami'in wanda ya bayyana hakan a jiya Alhamis ya kuma danganta karuwar abubuwa masu gurbata muhalli da ake fitarwa a nahiyar kan rashin wata doka game da yadda ake shigar da motocin da aka riga aka yi amfani da su cikin nahiyar.

De Jong ya kuma lura da cewa, gabilin kasashen nahiyar ba su da wasu manufofi game da yadda ake shigo da motoci kana manufofin da kasashen nahiyar ke amfani da su a halin yanzu suna cin karo da juna. Ya ce a shekarar 2014 kadai, kasashen Benin da Najeriya da Ghana da Kenya da Afirka ta Kudu da Tanzaniya da Guinea da Kamaru da Togo da Uganda sun shigo da sama da motoci miliyan 42 da aka riga aka yi amfani da su cikin kasashensu.

Ya ce duk da cewa, irin wadannan tsoffin motoci sun samar da damammaki, a hannu guda kuma suna haifar da kalubale kan yanayinsu da ma batun amfani da mai.

A don haka De Jong ya bukaci gwamnatocin kasashen Afirka da su yi kokarin samun fasashohin zamani masu sauki wandada za su taimaka musu samun motoci masu inganci da za su dace da yanayin kasashensu, kana ba su da wata illa a bangaren kudi, yanayi da kuma koshin lafiya.

Ya ce a shirye shirin kare muhalli na MDD yake ya taimakawa kasashen wajen tsara manufofi na bai daya. Ya kuma ba da shawarar cewa, kamata ya yi masu shigo da irin wadannan motoci su rika ba da gudummawar dala daya kan kowace motar da suka fitar don taimakawa wajen magance matsalar muhallin da suka haifar.

A cewar shirin kare muhalli na MDD, irin wadannan tsoffin motoci dake nahiyar, galibi an shigo da su daga kasashen Japan da kasashen Turai da kuma Amurka. An kuma yi kiyasin cewa, a kowace sherkara kasar Kenya ta kan shigo da kaso 96 cikin 100 na motocin da aka riga aka yi amfani da su, yayin da Najeriya ke shigo da kaso 99 cikin 100,Kasar Laberiya kaso 90 cikin 100. Sai dai tsoffin motocin da Uganda ke shigo da su sun dara sabbi. Yawancin motocin dai ana sayensu ne ta shafin Intanet.

Irin wadannan tsoffin motocin dai suna da farin jini a galibin kasashen Afirka, amma kuma yadda suke fitar da hayaki mai gurbata muhalli ya dara na sabbin motoci.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China