in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta gudanar da bikin tuna da ranar daji ta duniya
2018-03-22 11:08:22 cri
Ranar 21 ga wannan wata rana ce ta daji ta duniya ta 6 da MDD ta tabbata, takenta a bana shi ne "daji da birane mai dorewa". A wannan rana, biranen kasar Sin, ciki har da birnin Beijing sun gudanar da bikin tuna da ranar daji ta duniya.

A ranar 21 ga wannan wata, wakilai fiye da 200 na kwamitin kula da daji na kasar Sin da hukumar kula da sha'anin daji ta kasar Sin da sauran hukumomin kasar da kuma kungiyoyin kasashe da yankuna fiye da 10 sun halarci bikin shuka itace don tunawa da ranar daji ta duniya a garin Zhangfang dake unguwar Fangshan ta birnin Beijing, inda suka shuka itatuwa fiye da 700.

Mataimakin shugaban hukumar kula da sha'anin daji ta kasar Sin Liu Dongsheng ya bayyanawa 'yan jarida a gun bikin cewa, a nan gaba birane dake da itatuwa da dama suna da muhimmanci sosai yayin da ake raya sha'anin daji a kasar Sin. Mr Liu ya bayyana cewa,

"Ana bukatar biranen kasarmu da su kara mai da hankali ga sha'anin daji, akwai doguwar hanya wajen inganta sha'anin daji a fannonin muraba'insu da ingancinsu. Ana bukatar raya sha'anin daji a kasar Sin a dogon lokaci, baya ga shuka itatuwa a birane da kauyuka, muna son cimma burin mai da yawan daji da aka samu a kasar ya kai kashi 23 cikin dari a shekarar 2020, da kuma yawansu ya kai kashi 26 cikin dari a shekarar 2035, don haka ana bukatar mu kara shuka itatuwa da dama a nan gaba."

An ce, a shekarun baya baya nan, Sin tana kokarin inganta sha'anin daji a birane da kauyuka, da sa kaimi ga gina birane dake da itatuwa da dama a yankunan Beijing, Tianjin da Hebei, Delta kogin Yangtse, Delta kogin Zhujiang da sauransu, da mai da yawansu ya kai 137 a dukkan kasar Sin.

Bayan shekarar 2013, Sin ta gudanar da bikin shuka itatuwa don tuna ranar daji ta duniya a birnin Beijing a shekaru 6 a jere, mashawarciyar ofishin jakadancin kasar Canada dake kasar Sin Angela Graham ta halarci bikin a bana da bayyanawa 'yan jarida cewa, ta gano gwamnatin kasar Sin ta dora muhimmanci ga aikin kiyaye muhalli da shuka itatuwa. Ta ce,

"Babu shakka na ga ingancin iska na lokacin hunturu da ya gabata ya fi kyau bisa na shekarun baya, a ganina manufofin gwamnatin kasar Sin sun yi tasiri a wannan fanni, ana kyautata yanayin kasar. Kana kasar Sin ta fara kyautata aikin kiyaye muhalli, wanda ya kawo tasiri ga dukkan duniya gaba daya, na yi farin ciki sosai game da hakan."

A wasu shekarun da suka gabata, kasar Sin ta gudanar da ayyukan sa kaimi ga jama'a da su shuka itatuwa ta hanyar internet a birnin Beijing, da yankin Mongoliya cikin gida, da lardin Anhui, da lardin Shaanxi da sauran wuraren kasar, wadanda suka samu nasarori. Shugaban sashen sarrafa sha'anin daji na kwamitin kula da daji na kasar Sin Pan Bing ya yi bayani cewa, akwai hanyoyi da dama ga jama'a da suka halarci aikin shuka itatuwa. Ya ce,

"Bisa ka'idojin da aka tsara, ya kamata kowane mutum na kasar Sin ya halarci aikin shuka itatuwa ko sauran aikin dake shafar wannan fanni a kowace shekara. A shekarar bara, kwamitin kula da daji na kasar Sin ya gabatar da ka'idojin shuka itatuwa a dukkan fannoni, jama'a suna iya halartar ayyukan dake shafar fannin ta hanyoyi 8, ciki har da shuka itatuwa, da kula da itatuwan da aka shuka a lokacin baya, da ba da kudin kyauta ta hanyar internet, da tabbatar da tsaron tsofaffin itatuwa, da shiga aikin kiyaye daji da sauransu, wadannan hanyoyi sun dace da halin da ake ciki a kasar." (Zainab)


Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China