180320-FOCAC-Kande.m4a
|
Jakada Zhou Yuxiao mai kula da harkokin taron dandalin tattaunawar hadin kai tsakanin Sin da Afirka na FOCAC ya bayyana Jiya Litinin a Nairobi, hedkwatar mulkin kasar Kenya cewa, za a kira taron koli na Beijing na dandalin FOCAC a watan Satumbar bana, inda batun "hada shawarar 'Ziri daya da hanya daya', da ajandar kungiyar AU ta shekarar 2063, da tsare-tsaren ci gaban kasashen Afirka, domin kara inganta hadin gwiwar Sin da Afirka" zai zama babban takensa.
Jakada Zhou Yuxiao ya fadi hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai na Sin da Kenya. A kwanakin baya, jakada Zhou da kwararru da masana na hukumar nazari kan hadin gwiwar Sin da Afirka, sun ziyarci kasashen Habasha da Uganda da kuma Kenya, inda suka tattauna da jami'ai da masana na kasashen uku, kan babban taken taron koli na Beijing na FOCAC da kuma abubuwan da za a tattauna a yayin taron.
Yayin da yake tabo batun yadda aka aiwatar da manyan ayyuka goma na hadin gwiwar Sin da Afirka da aka gabatar a yayin taron koli na Johannesburg na dandalin FOCAC, jakada Zhou ya bayyana cewa,
"Bisa kokarin da bangarorin Sin da Afirka ke yi, yanzu ana aiwatar da manyan ayyuka goma na hadin kansu yadda ya kamata. A fannin manyan ayyukan more rayuwar jama'a, an riga an kammala wasu ayyukan da ke shafar layin dogo da tashar jiragen ruwa da filin jiragen sama, yayin da wasu daban ke gudana lami lafiya. Bugu da kari, an samu babban ci gaba dangane da wasu ayyukan da ake shiryawa."
Ban da wannan kuma, jakada Zhou ya furta cewa, yanzu Sin da Afirka na kyautata hadin kansu a fannonin da suka shafi al'adu da ilmi da matasa da mata. Ya kara da cewa,
"A cikin wadannan shekaru biyu da suka gabata, kasar Sin ta taimakawa kasashen Afirka wajen horar da masu fasaha kimanin dubu 150 a nahiyar, yayin da ta samarwa masu fasaha da jami'an Afirka dubu 30 kwasa-kwasan samun horo a kasar Sin, baya ga yadda ta samar wa daliban Afirka dubu 20 kudin karatu don karo ilminsu a kasar Sin. Kawo yanzu dai, an riga an samu babban ci gaba wajen yin amfani da kashi 70 cikin dari na kudin dala biliyan 60 da kasar Sin ta alkawarta samarwa cikin manyan ayyukan goma. A shekara mai zuwa ma, kasar Sin za ta ci gaba da kokari don gudanar da ayyukan da sauran kudin."
Abin da jakada Zhou ya fi dora muhimmanci wajen yin magana a kai shi ne, babban taken taron koli na Beijing na FOCAC da za a yi a watan Satumbar bana, wanda za a hada shawarar "Ziri daya da hanya daya", da ajandar kungiyar AU ta shekarar 2063, da ma tsare-tsaren ci gaban kasashen Afirka daban daban gaba daya. Yana mai cewa,
"Da farko dai, muna ganin cewa, shawarar 'Ziri daya da hanya daya' za ta zama babban taken taron koli na Beijing na FOCAC. Za mu duba yadda za a hada shawarar tare da ajandar AU ta shekarar 2063 da ajandar samun dauwamammen ci gaban ta MDD ta shekarar 2030 da ma tsare-tsaren ci gaban kasashen Afirka daban daban gaba daya. Yanzu kasar Sin na da burin da take son cimmawa, kasashen Afirka ma na da na su burin, ana iya hada burikan kasar Sin da na kasashen Afirka tare. Na yi imanin cewa, bangarorin biyu za su iya cimma burinsu ta hanyar gudanar da ayyukan hadin kai iri daban daban a inuwar tsarin FOCAC."
Har ila yau, jakada Zhou ya furta cewa, yanzu kasar Sin ta riga ta samar wa kasashen Afirka dimbin kwasa-kwasan horo, kamar "shirin hadin kai a tsakanin jami'o'in Sin 20 da na Afirka 20", da "shirin hadin kai a tsakanin hukumomin nazarin kimiyyar ayyukan gona na Sin 10 da na Afirka 10". Ya na mai cewa, a nan gaba ma, kasar Sin za ta ci gaba da gudanar da ayyukan da abin ya shafa, a kokarin habaka hadin gwiwar bangarorin biyu.(Kande Gao)