An rufe taron farko na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 13 a yau 20 ga wata a nan birnin Beijing, inda shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin wato NPC na wannan karo Li Zhanshu ya bayyana cewa, tunanin shugaba Xi Jinping game da tsarin mulki na gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin a sabon zamani da ake ciki tunani ne dake jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin a dogon lokaci, kana shi ne tunanin dake jagorancin kasa da aka tabbatar bisa gyaran kundin tsarin mulkin kasar. Tilas ne a tsaya tsayin daka kan tunanin jagorancin kasar da aka tabbatar bisa kundin tsarin mulkin kasar.
A gun taron na kwanaki 16, an kammala aikin gyara kundin tsarin mulkin kasar, da tattaunawa da zartas da dokar sa ido, da shirin yin kwaskwarima kan hukumomin majalisar gudanarwar kasar, da dubawa tare da zartas da rahoton aikin gwamnatin kasar da sauran rahotannin hukumomin kasar, da zaba da kuma nada sabbin shugabannin gwamnatin kasar. (Zainab)