in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Sin da takwaransa na Rasha sun taya juna murnar sabuwar shekara
2016-12-31 18:02:26 cri
A yau Asabar, Shugaban Sin Xi Jinping da takwaransa na Rasha Vladimir Putin sun mika sakon taya murnar sabuwar shekara ga juna.

Shugaba Xi Jinping ya nuna cewa, kyakkyawar dangantaka da hadin kan dake tsakanin Sin da Rasha, ta taka muhimmiyar rawa wajen samar da zaman lafiya da ci gaba a yankinsu da ma duniya baki daya.

A sakon na sa, Shugaban na Sin, ya ce a shirye yake, ya ci gaba da hada hannu da Shugaba Putin, wajen musayar bayanai, da kara aminta da juna wajen inganta nahiyarsu da karfafa kawacen Turai da yankin Asia kan tattalin arziki.

Shi ma a nasa sakon, shugaban Rasha Vladimir Putin, ya taya shugaba Xi murnar sabuwar shekara.

Vladimir Putin ya ce kasashen biyu sun aiwatar da kuduri na uku dake karkashin yarjejeniyar hadin kai ta zumunci ta makwabta dake tsakaninsu, haka zalika, sun yi nasarar warware matsaloli da ya shafi yankinsu da ma duniya baki daya.

Shugaba Putin ya ce ya yi imanin cewa, cikin sabuwar shekara da za a shiga, dangantakar dake tsakanin kasashen, za ta kara armashi, ta yadda al'ummominsu za su kara amfana, sannan, ya taimaka wajen wanzar da tsaro da zaman lafiya. ( Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China