Ya ce, ban da haka, kasar Sin za ta iya kara zuba jari domin kyautata fasahohin zirga-zirga a cikin biranen nahiyar Afirka gami da tsakaninsu. Sa'an nan bisa shawarar "ziri daya da hanya daya" da kasar Sin ta gabatar, kasar za ta samu damar zuba jari ga aikin shimfida layin dogo irin na karkashin kasa a biranen Afirka, gami da tsarin zirga-zirga mai alaka da makamashi mai tsabta.
An kebe "makon zirga-zirga ba tare da gurbata muhalli ba" da nufin saukakawa jama'ar nahiyar Afirka harkokin zirga-zirga. Jami'an gwamnatoci, da masu kamfanoni, da masana na wasu kasashen dake nahiyar Afirka kimanin 40 sun halarci taron na wannan karo.(Bello Wang)