in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Habasha ta jinjinawa muhimmacin layin dogo da ya hada kasar da Djibouti
2018-03-15 10:41:33 cri
Daraktan kamfanin dake kula da layin dogo na zamani da kasar Sin ta gina, wanda ya hada Habasha da kasar Djibouti Tilahun Kassa, ya jinjinawa muhimmancin dake tattare da layin dogon, watanni biyu bayan fara amfani da shi.

Da yake bayyana nasarorin da aka cimma tun bayan bude harkokin sufurin jiragen kasa ta layin dogon mai aiki da lantarki, Mr. Kassa ya ce layin ya hada Habasha dake tudu da kasar Djibouti mai iyaka da teku. An kuma yi sufurin kwantenoni na dakon kaya sama da 2,000 cikin wadannan watanni biyu.

Jami'in ya kara da cewa, akwai alamu da ke nuna za a cimma gagarumar nasara, ta fuskar fadada hada hadar fitar da kayayyaki, da cinikayya daga Habasha zuwa sauran kasashen duniya ta wannan sabon layin dogo.

An dai kaddamar da layin dogon wanda kamfanin kasar Sin ya gina mai tsawon kilomita 756 a farkon wannan shekara da muke ciki. Ana kuma fatan zai ba da damar dakon kwantainoni 106 a zango guda na sufuri.

Kaza lika layin dogon ya rage tsawon lokacin zirga zirga tsakanin kasashen biyu, daga kusan kwanaki 3 zuwa kasa da sa'oi 12. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China